Hukumar EFCC a Najeriya ta kama mutum 140 da ake zargi suna damfara ta Intanet wanda ake kira “yan yahoo” a wani otel da ke Legas.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar, Mista Wilson Uwujaren, ya ce mutanen masu shekara tsakanin 16 zuwa 42, an kama su ne a wasu otel biyu da ke yankin Ikorodu.
Uwajaren ya ce kamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan ayyukan da suke aikatawa na kutse da damfara a shafukan Intanet.
Abubuwan da aka kama matasan da su sun hada da motocin alfarma da naurorin laturoni da kamfutoci da kuma wayoyin hannu.
Za a gabatar da matasan a gaban kotu nan bada jimawa ba, a cewar jami’in.