An gurfanar da tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke ABU, Farfesa Ibrahim Garba da Ibrahim Usman a gaban kotu bisa zargin zamba.
A ranar Laraba ne aka gurfanar da tsoffin jami’an a gaban mai shari’a R. M. Aikawa na babbar kotun tarayya da ke jihar Kaduna.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da su da laifuffuka tara da ke da alaka da almundahanar kudade sama da Naira biliyan daya.
Karanta Wannan: Gwamnatin Legas ta gurfanar da Malaman makaranta da zargin kashe ƴar shekara 12
Ana tuhumar su ne da karkatar da kudaden da aka tanada, domin gyaran babban otal din Kongo Conference Hotel da ke Zariya.
Laifin, wanda aka aikata wani lokaci a cikin Disamba 2013, ya saba wa Sashe na 18 (a), 15 (2) (d) na Dokar Hana Balaguron Kudi, 2011 (kamar yadda aka gyara).
Garba da Usman sun amsa cewa ‘ba su da laifi’ lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.
Lauyan da ya shigar da kara, Jamil Musa, ya bukaci kotun da ta tsare su a gidan gyaran hali na Kaduna tare da sanya ranar da za a fara shari’ar.
Lauyan kare, M.S. Aatu, SAN, ya bukaci kotu da ta shigar da wadanda yake karewa don bayar da belinsa.
Mai shari’a Aikawa, ya bayar da belinsu a kan kudi Naira miliyan 5 tare da mutum daya wanda zai tsaya masa, ba kasa da mataki na 15 a ma’aikatan gwamnati ba.
Dole ne wadanda ake tuhuma su ajiye fasfo dinsu na kasa da kasa a gaban kotu sannan su kai rahoto ga EFCC duk ranar Litinin ta farkon wata.
Mai shari’a Aikawa ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 20-21 ga watan Yunin 2023 domin sauraren karar.