fidelitybank

EFCC ta gurfanar da Stella a kan harƙallar kuɗaɗe

Date:

Hukumar Yaki da cin hanci da yi wa tattalin arziki Ta’annati EFCC, ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya Stella Oduah, tare da wasu mutum takwas a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin almundahanar kuɗaɗe.

An gurfanar da mutanen ne kan zarge-zarge 25 da suka haɗa da halasta kuɗin haram, da haɗin baki, tare da amfani da wani asusun ajiyar banki marar suna a bankin First Bank da aka samu kimanin naira biliyan biyar a cikinsa.

Sai dai bayan karanto musu zarge-zargen Oduah tare da sauran mutanen takwas ciki har da wata tsohuwar hadimarta, sun musanta duka zarge-zargen da hukumar ke yi musu.

Alkalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo ya umarci ofishin babban Atoni-Janar na ƙasa da ya karbi hurumin shigar da ƙarar daga hannun hukumar ta EFCC.

Stella Oduah ta riƙe muƙamin ministar sufurin jiragen sama a lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan tsakanin shekarar 2011 zuwa 2014.

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...
X whatsapp