Hukumar EFCC, mai yaƙi da almundahana a Najeriya ta gurfanar da wata mata da mijinta bisa zargin sojan gona da sunan mai ɗakin gwamnan jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda domin damfar kuɗin da suka kai naira miliyan 197,750,000.
EFCC ta gurfanar da su a gaban babbar kotun jihar Kaduna tare da wasu mutum biyu da ke taimaka musu wajen gudanar da mugunyar sana’ar.
Hukumar ta zargi mutanen huɗu da haɗin baki wajen damfarar waɗannan kuɗaɗe ta hanyar fakewa da sunan mai ɗakin gwamnan Katsina, da nufin neman canjin dala.
EFCC ta zargi matar da ayyana kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, inda take buƙatar a yi mata canjin dala, daga wani mai sana’ar canji.
Mijin nata, ya samar mata da layukan waya da aka yi wa rajista da sunan Fatima Dikko Radda, domin ɓad-da-bami ga manhajar ‘True Caller’ da ke gano sunan mai lambar waya, a cewar EFCC.
Bayan ta buƙaci yi matan canjin dalar ne, sai suka tura wa mai canjin lambar asusun ajiyar da zai tura kuɗin kafin ta aika masa da dalar, kamar yadda hukumar ta bayyana.
EFCC ta ce da farko matar, ta karbi naira miliyan 89 daga wani mai suna Aminu Usman da nufin tura masa dala 53,300.
Daga baya kuma ta sake karɓar naira miliyan 108 da nufin canja mata dala 118 da ta ce za ta aika masa, kamar yadda EFCCn ta bayyana.