Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta gurfanar da tsohon magatakardar Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Zamfara 1, Gusau, Abubakar Garba Dandare, a gaban Mai Shari’a Bello Shinkafi na Babbar Kotun Jihar Zamfara da ke Gusau.
Hukumar ta gurfanar da Dandare ne a kan tuhume-tuhume biyu, inda ta zarge shi da karkatar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 3.8 na wani dan kasuwa marigayi Alhaji Ladan Mada da kuma jabun sa hannun makusancinsa, Aminu Mada.
A cikin karar mai lamba ZMJ/GS/13C/2024, Dandare an tuhumi shi ne da laifin karkatar da N3,837,634.46, wanda ma’aikatar kudi ta jihar Zamfara ta bashi amanar iyalan marigayi Alhaji Ladan Mada a watan Disambar 2012, lokacin yana magatakardar hukumar. Upper Sharia Court 1, Samaru Gusau, Zamfara State.
An kuma zargi Dandare da yin jabun sa hannun Aminu Mada, dan gidan marigayi Alhaji Mada, a rajistar ajiyar kudi na kotun shari’a ta 1, Samaru Gusau, jihar Zamfara, da nufin samun kudaden.
Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, matakin ya kunshi laifukan cin amana, kamar yadda aka bayyana a sashe na 311 da 312 na Penal Code, CAP 89 Laws of Northern Nigeria, 1963.
Mai shari’a Bello Mohammed Shinkafi ya bayar da belin wanda ake tuhuma, bisa sharadin ya bayar da wadanda za su tsaya masa guda biyu mazauna jihar, a kan kudi naira miliyan biyar.
Kuma dole ne su mika fasfo dinsu da lambobin GSM guda biyu ga magatakardar kotu