A ranar Laraba ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a Abuja, ta bi umurnin babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja kan shari’ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
Emefiele wanda ya shafe sama da kwanaki 150 a hannun hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya an gurfanar da shi a gaban kotu bisa bin umarnin mai shari’a Olukayode Adeniyi.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin na CBN wanda ya sa rigar Babariga mai launin rawaya da hular Hausa don daidaitawa ya shiga harabar da misalin karfe 12:30 tare da wasu jami’an EFCC da ke ba da tsaro a kusa da shi.
Abokansa da ’yan uwansa sun yi wa harabar kotun kawanya suna jiran isowar alkali domin sauraren shari’ar sa na kare hakkin bil adama.
Mai shari’a Adeniyi a ranar Litinin din da ta gabata ya sake tabbatar da umarninsa na cewa a gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin na CBN a kotu a yau 8 ga watan Nuwamba domin bada belinsa.
Ya kuma umurci hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kanta da ta bayar da belin Emefiele ko kuma ta bar kotu ta yi hakan kamar yadda doka ta tanada kan hakkin dan adam.


