Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da wani ɗan ƙasar Indiya mai suna Chandra Prakash Singh, a gaban wata kotu da ke jihar Legas saboda zargin satar kuɗi da ya kai $ 200,000.
Hukumar ta ce a ranar 16 ga watan Disamban 2020 wanda ta ke zargin ya cire kuɗi $90,000 daga wasu asussa na bankin da ba mallakinsa ba wanda kuma ya saɓawa doka.
Sai dai wanda ake zargi ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.
Karanta Wannan: EFCC ta kama mutane a Kano da Abuja da Kaduna
A don haka ne, lauya mai gabatar da ƙara B.B Bala ya bukaci da a ci gaba da tsare shi, har sai an sake saka ranar ci gaba da sauraron shari’ar.
Sai dai lauya mai kare wanda ake ƙara, Efe Solomon Izokor, ya roki kotu da ta ba da belin wanda ake zargi.
Amma Barrister Bala ya bukaci lauyan da ya rubuta bukatar neman belin sannan ya kawo ta gaban kotun domin ba ta damar amsawa yadda ya kamata.
Mai shari’a Oweibo ya ɗage zaman sauraron karar zuwa 27 ga watan Yunin 2023.