fidelitybank

EFCC ta gurfanar da AA Zaura na jam’iyyar APC

Date:

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya zagon ƙasa ta gurfanar da ɗan takarar Majalisar Dattawa na Kano ta Tsakiya na jam’iyyar APC, AA Zaura a kotu.

EFCC ta gurfanar da ɗan takarar ne wanda cikakken sunansa shi ne Abdulsalam Abdulkarim Zaura a gaban wata babbar kotun tarayya a Kano a yau Laraba 1 ga watan Maris, 2023 a bisa zargin laifuka huɗu da suka danganci zamba.

A ɗaya daga cikin laifukan da aka karanta masa a kotun wadda mai shari’a Mohammed Nasir Yunusa ya jagoranta, an zarge shi da cewa a wani lokaci a watan Agusta na 2014, ya karɓi dala dubu 200 daga Dr Jamman Al- Azmi a kano, da nufin zamba, da karyar za su yi wata harkar kasuwanci ta haɗin gwiwa

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, bayan lauya mai gabatar da ƙara Aisha Tahar Habib ta karanta masa.

Lauyan AA Zauran, Ishaq Mudi Dikko,( SAN) ya nemi kotu ta bayar da belin wanda yake karewa, inda bayan ‘yar taƙaddama, alkalin kotun, Justice Yunusa ya amince da belin.

Yanzu dai an ɗage shari’ar har zuwa ranar 2 ga watan Mayu na 2023 domin fara saurare.

Za a fara shari’ar ne tun daga farko bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta soke saki da kuma wanke wanda ake zargin a kan laifin zamba da alkalin babbar kotun tarayya a Kano A. L. Allagoa ya yi a baya.

Ana zargin A.A Zaura da zambatar wani ɗan ƙasar Kuwait dala miliyan 1,320,000, a kan cewa shi ɗan kasuwa ne da ke harkar gidaje a Dubai da Kuwait da kuma wasu ƙasashen Larabawa.

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp