A wani yunkuri na dakile sayen kuri’u a zaben gwamnan jihar Osun, jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bayyana a wajen.
Rahotanni sun ce jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun isa filin shakatawa na Freedom, Old Garage, Osogbo, babban birnin jihar da misalin karfe 8 na safe.
Yayin da dukkanin ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban ke fatan lashe zaben gwamna, jami’an hukumar EFCC sun dukufa wajen rage sayan kuri’u da kuma tabbatar da an gudanar da sahihin zabe.