Jamiāan rundunar shiyyar Makurdi na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun cafke wasu mutane biyar da ake zargi da damfarar yanar gizo a babban birnin Makurdi, jihar Benue.
An sanar da hakan ne a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa da hukumar yaki da cin hanci ta X.
Sanarwar ta ce an kama su ne a ranar Alhamis din da ta gabata biyo bayan sahihan bayanan sirri kan zargin su da aikata laifukan da suka shafi intanet.
Wadanda ake zargin a cikin sanarwar sun hada da Stanley Tochukwu, Desmond Tochukwu, Dennis Emeka, George Ebuka da Arinze Odo.
EFCC ta bayyana cewa an kwato wasu kayayyaki da suka hada da wayoyi, bankin wuta, katin ATM da wasu kudade daga hannun wadanda ake zargin.
Ya kuma kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.