Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, reshen shiyyar Kaduna, ta kama wasu mutane 48 da ake zargi da damfara.
Hukumar ta kuma kama wasu mata biyu Precious Malachi Zidyep da Tina Patrick Omoyeme a Otal din Rosalux Blue dake Agua a Kaduna ta Kudu a wani samame da ta kai Kaduna.
Wadanda ake zargin sun kuma hada da wasu tsofaffin mutane biyu: Williams Justice Gankon da AbdulWasiu Yunus wadanda a baya aka kama su a ranar 10 ga Afrilu, 2022, aka gurfanar da su a gaban kotu kuma aka yanke musu hukunci a ranar 31 ga Agusta, 2022 daga hannun mai shari’a Nasiru Umar Sadiq na babbar kotun jihar Kaduna.
An kama su ne a titin Yoruba, babban titin Yakowa, Karji, jihar Kaduna.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da wayoyin hannu na samfura daban-daban da kwamfutocin laptop.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.