Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Abuja, ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da damfarar yanar gizo a Kubwa, Abuja.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce an samu gagarumin ci gaba a yakin da take yi da aikata laifuka ta yanar gizo a aikin ta na baya-bayan nan a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook.
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin sune Favour Obinna, Chinaza Onuigbo, Abdulrahman Ibrahim, Suleiman Daude, Ali Daude, Godwin Ifeanyi, Victor Ageme, Enoch Alfa, Wisdom Ndubuisi, Matthew Gideon, Stanly Kosi, Japhet Akogun, James Efegha da Christopher Enaho.
Sauran, sanarwar ta ce, Daniel Benjamin, Idris Salvation, Idris Victor, Ikechukwu Ephraim Idris, Abdullahi Sani, Jeremiah Yacim, Chindu Chukwuma, Mohammed Daude Hamisu, Tochukwu Trust, Theophilus Marshal, Sani Solomon da Chukwu Nnaemeka Oscar.
Ta kuma bayyana cewa, a yayin gudanar da aikin, EFCC ta kwato mota kirar Toyota Camry SE, Mercedes Benz GLK 350, da Lexus IS guda biyu motoci 250, da kuma wayoyin hannu da kwamfutoci da dama daga hannun wadanda ake zargi da damfarar yanar gizo.
Sanarwar ta ce wadanda ake zargin za su fuskanci tuhuma da zarar hukumar ta kammala bincike.