Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a Jihar Akwa Ibom, sun kama wasu dalibai 19 na Jami’ar Jihar Akwa Ibom, Mkpat-Enin da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi intanet.
An kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a a gidajen kwanan su na Obong Abasi Lodge da Mfon Obong Lodge da ke Ikot Akpadem a karamar hukumar Mkpat-Enin a jihar Akwa Ibom.
An zargi wasu daga cikin wadanda ake zargin da hannu a badakalar soyayya, da zamba ta mu’amalar cryptocurrency da kuma kwaikwaya.
An kwato wasu kwamfutoci da wayoyin hannu da dama daga cikinsu.
Hukumar ta kara da cewa za ta gurfanar da daliban gaban kotu da zarar an kammala bincike.