Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Laraba, ta kama wasu mutane goma sha daya da ake zargi da damfarar yanar gizo mai suna “Yahoo boys” a jihar Borno.
Jami’an rundunar shiyyar Maiduguri sun kai wani samame a kananan hukumomin Jere da Maiduguri.
Wadanda ake zargin sun hada da Micah Joseph, Mari Ayuba, Ibrahim Abdullahi, Adam Abiodun da kuma Victor Chinonso Okolieaboh.
Sauran sun hada da Olatunji Sherif, Bright Felix, Jude Linus Magaji, Jonah Jondi, Ojobaro Abdullahi, da Jerry Zizighi,
An kama su ne biyo bayan sahihan bayanan sirri kan aikata laifukan da ake zarginsu da aikatawa, a cewar shugaban yada labarai na EFCC, Wilson Uwujaren.
An gano wata Mercedes Benz GLK 350, mota kirar Toyota Corolla saloon, wayoyin komai da ruwanka, na’urar Wi-Fi, da bankunan wuta.
Uwujaren ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.