Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta kama wasu mutane 18 da ake zargi da damfarar yanar gizo, wadanda aka fi sani da “Yahoo boys” a unguwar Lekki da ke jihar Legas.
Kakakin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Wilson Uwujaren, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, an kama wadanda ake zargin ne, biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu kan zarginsu da hannu wajen damfarar kwamfuta.
Sanarwar ta bayyana wadanda ake zargin sun hada da: Tijani Olumide Ahmed, Balogun Olusola, Ukuhor Richie Ifemeluona, Ologun Damilola, Adetokunbo Yusuf, Olubiyo Timilehin, Oyegoke Gafar Olaitan, Agarawu Faruq Okikiola, Kazeem Oluwadamilare Adebayo da kuma Salau Rahmon.
Sauran sun hada da: Abdulrahman Adeshina Olasunkanmi, Rasheed Remilekun, Adeyanju Kehinde Emmanuel, Owolabi Temidayo Habeeb, Ojora Usman Olawale, Mubarak Balogun, Rafiu Olusegun da Ayobami Habeeb Oyeleye.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin a cewar EFCC, sun hada da, motoci, kwamfutoci, wayoyin hannu da kuma layu.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bayan an kammala bincike.