Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na shiyyar Abuja sun kama wasu mutane 29 da ake zargi da damfarar yanar gizo a ranar Laraba.
An kama wadanda ake zargin ne a unguwar Apo, Gwarimpa da Katampe a Abuja.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce kama su ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da zargin da ake musu na damfara ta intanet.
Kayayyakin da aka kama daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyi 43 na kera daban-daban, motoci shida da agogon smart guda biyu.
ya kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.