Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Larabar da ta gabata sun kama wani tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.
Wasu ‘yan bindiga ne suka dauke shi daga gidansa da ke Abuja.
An cafke farfesa a fannin ilimin haifuwa da cutar sankarau da dashen kasusuwa a gaban matarsa da ‘ya’yansa da misalin karfe 4:46 na yamma bisa wani laifi da ba a bayyana ba tukuna.
An kai Yusuf inda ba a sani ba.
Jami’an ba su bayyana yadda aka kama shi ba, amma kamun nasa ba zai rasa nasaba da ayyukansa ba a lokacin da yake rike da mukamin NHIS.
Wata majiya ta bayyana cewa, “Ba za a iya bayyana dalilin kama shi a yanzu ba saboda ana ci gaba da bincike. Abin da na sani shi ne yana tsare kuma zai taimaka wa masu binciken a bincikensu.”
A shekarar 2019 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke Yusuf daga mukaminsa watanni bakwai bayan da kwamitin bincike da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta kafa kan badakalar N919m ya ba shi shawarar korar sa.


