Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a Gombe, sun kama Zachariya Muhammad da laifin watsa takardar Naira, al’adar da ake ganin tamkar cin zarafi ne da kudin Najeriya.
Kamen dai ya biyo bayan bayanan sirri da ke alakanta Muhammad da aikata laifin, wanda ya faru a G-Connect da ke Tunfure a Gombe.
Hukumar EFCC ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gano Muhammad ne a wani faifan bidiyo inda aka gan shi yana rawa yana feshin kudi Naira 200.
A cewar sanarwar, Muhammed ya amince da cewa shi ne mutumin a cikin faifan bidiyon da aka yi masa tambayoyi.
“Bayan kama shi, an nuna masa wani faifan bidiyo inda yake rawa yana fesa takardar Naira a kan Naira Dari biyu (N200). Ya yarda cewa shi ne a cikin bidiyon.
Sanarwar ta ce “Za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.”
Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) musamman sashe na 21, ta yi Allah wadai da cin zarafin Naira daban-daban da suka hada da tafka magudi, tada zaune tsaye, yaga, feshi, da shawa.
Dokar ta tanadi hukuncin daurin akalla watanni shida a gidan yari ko kuma tarar da ta fara daga N50,000 ga wadanda suka aikata laifin.
Karamin sashe na (3) ya fayyace cewa fesa ko rawa a kan takardun naira a lokutan bukukuwan zamantakewa laifi ne da za a hukunta shi a karkashin karamin sashe na (1).
Ku tuna cewa a kwanakin baya ne EFCC ta bi wasu fitattun mutane da ake zargin suna zagin Naira.
A ranar 12 ga watan Afrilu wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta yanke wa fitaccen jarumin dandalin sada zumunta, Bobrisky hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, bisa samunsa da irin wannan laifin.
A farkon watan Mayu ne dai hukumar EFCC a Kano ta samu hukuncin dauri kan wasu mutane 31 da ke da hannu a hada-hadar kudaden haram da kuma karkatar da naira.