Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ta kama wasu mutane tara da ake zargi da damfarar mutane ta yanar gizo a Abuja.
Wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da wayar da kan jama’a, Wilson Uwujaren, ya fitar a ranar Laraba, ta ce an kama su ne a wani samame da aka kai musu.
Wadanda ake zargin dai su ne Bassey Sunday Junior, Samson Zakariah, Ogonyi Jeremiah, da Sunday Martins.
Sauran sun hada da Austin Yayison, Wilson Chinaza, Emmanuel Adeyi, Samuel Mark, da Emmanuel Bassey.
An kama su ne a ranar Talata, 30 ga watan Agusta a otal din Voque da ke Unguwar Mararaba a Abuja bisa zargin su da aikata laifuka ta yanar gizo.
An kwato wayoyi goma sha uku, kwamfutoci uku, da akwatin kida na Harman/Kardon daga hannunsu.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.


