Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a ranar Alhamis, ta kama wasu mutane 8 da ake zargi da damfarar yanar gizo a Abuja.
An kama wadanda ake zargin ne a Kubwa da Mararaba dake makwabtaka da jihar Nasarawa.
An bayyana sunayensu da David Oche Igoche, Innocent Adikwu, Anderson Oshiomegie Edemode da Chinonso P. Peter.
Karanta Wannan: An kashe mutane 46 ciki harda ɗan shugaban ƙaramar hukuma a Benue
Sauran sun hada da Emmanuel Smart, Favour Anucha, Adegbayi Tunde da Desmond Esosa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma bayyana cewa, an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu.
An kwato sama da wayoyin hannu biyar, kwamfutar tafi-da-gidanka 2 da na’urorin haÉ—in Intanet 2 daga hannunsu.
Hukumar ta kara da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.