Jami’an rundunar shiyyar Enugu na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, sun kama wasu mutane 32 da ake zargi da damfarar yanar gizo a wani samame da suka yi a lokaci guda a Awka, jihar Anambra da kuma garin Enugu na jihar Enugu.
Wadanda ake zargin sun hada da Stanley Okechukwu, Chukwudi Michael, Nnaife Onyedika, Nnamdi Christian, Pascal Akachukwu, Ekeme Christian Luke, Denis Chidozie da Ebuka Mmaduka.
Sauran sun hada da: Ekene Excellent, Emmanuel Okochi Osita, Akunne Prince Ikenna, Igwe Nnaemeka Shedrack, Nonso Henry Ozo Ekwe, Ebuka Obike Boniface, Goodluck Ameachi Ifeanyi, Hillary Chiemele Chukwudizie, Chinedu Onwuegbusi Ignitus, Onuoha Ifeanyi Anthony.
Sauran sun hada da: Bassey Nnolue Jason, Chinedu Nnolue Kingsley, Okpe Matthew, Emmanuel Abonyi, Igwenagu Kenechukwu Collins, Joachim Okpe, Kelechi Ibenyenwa, David Chiemerie, Kingsley Ngwu, Ndubuisi Anthony, Collins Chidubem, Innocent Chisom, Kalu Nnachi da Chukwuemeka Henry.
An kama su ne bisa wasu sahihan bayanan sirri kan ayyukan da ake zarginsu da aikata laifukan da suka shafi intanet.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sune wayoyi, kwamfutoci da motoci biyu: Lexus ES 350 da Lexus RX 330.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.