Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki ta EFCC, ta kama tsohon mai aikata zamba ta intanet tare da ƙarin wasu mutum 17 bisa laifin zamba ta intanet.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ofishin hukumar reshen Ibadan ne ya gurfanar da mutanen a gaba kotu.
Kotun dai ta same su da laifi, inda ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.