Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa EFCC shiyyar Ilorin tare da haɗin gwiwar tawagar sintiri ta hukumar hana fasa ƙwauri, sun kama wasu mutuane 18 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar EFCC ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta na X a yau.
Ta ce, sun kuma kama manyan motoci 13 ɗauke da ma’adinai iri-iri da ake zargin sun haɗa da Lithium da duwatsu masu daraja da farar hoda da dai sauran su tare da ƙwato su daga hannun waɗanda ake zargin.
An kama wasu cikin waɗanda ake zargin ne a ranar Talata, yayin da kuma aka kama wasu mutane uku a ranar Alhamis.
Kamen na zuwa ne bayan samun bayanan sirri kan ma’adinai da aka haƙo ba bisa ƙa’ida ba, da isar da su ta hanyar Eiyenkorin da Ballah a karamar hukumar Asa ta jihar Kwara, ba tare da wata doka ba.
EFC ta ce, za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken da ake yi.