Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta cafke MD/CEO na Marvelrock Pharmaceuticals and Stores Limited, Orakwe Chibuike Celestine.
An kama Celestine ne a babban birnin tarayya, bisa laifin yin cinikin haramtattun kwayoyi da sarrafa su a dandalin kasuwanci na intanet.
Wanda ya kammala karatun Business Administration a Jami’ar Abuja ya yi wa kamfanin harhada magunguna rajista a ranar 16 ga Disamba 2014.
An yi rajistar tare da takardar shaidar da goyon bayan wani mai lasisin magunguna, wanda ya fice daga yarjejeniyar a cikin 2017.
Amma wanda ake zargin ya ci gaba da gudanar da sana’ar tare da shigar da ita a dandalin yanar gizo a shekarar 2019, kamar yadda kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Laraba.
An fara sa ido kan Celestine a watan Oktoba 2021 lokacin da ya tallata kayayyaki irin su Tramadol, allurar Ketamine Hydrochloride, Allunan Hypnox flunitrazepam, da sauransu, akan intanet.
Tsakanin 26 ga Oktoba 2021 zuwa 8 ga Agusta 2022, tawagar jami’an hana shan miyagun kwayoyi da aka sanya wa shari’ar sun tabbatar da cewa yana sayar da Tramadol 225mg da sauran magunguna ta yanar gizo.
“An kama wanda ake zargin dauke da wasu nau’ikan Tramadol da Swiphnol na Rohypnol a ranar Litinin 8 ga watan Agusta a wata mashaya da ke unguwar Jabi a Abuja inda ya je yin wasu kayayyaki.”
Shugaban hukumar ta NDLEA Mohamed Buba Marwa ya ce, bincike da kama dan kasuwar ya kamata su aike da sako mai karfi ga masu amfani da yanar gizo wajen siyar da miyagun kwayoyi da hukumar za ta samu.


