Jamiāan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Ibadan sun kama mutane ashirin, 20 da ake zargi da damfarar yanar gizo.
Hukumar ta ce an kama wadanda ake zargi da damfara ne a ranar Laraba, 20 ga Maris, 2024, a unguwar Akobo da ke Ibadan.
Kamen nasu ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan ayyukansu na damfara da ke da alaka da intanet.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da manyan motoci guda goma, kwamfutocin tafi-da-gidanka goma sha biyu, wayoyin hannu arbaāin da daya(41), da PlayStation 5 daya, talabijin guda daya da sauran takardu na cin zarafi da sauransu.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara da cewa za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.


