fidelitybank

EFCC ta bankado Dala miliyan 72.8 a asusun tsohuwar Minista

Date:

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), ta sake bankado Dalar Amurka miliyan 72.8 a wani asusun ajiyar kudi na tsohuwar Ministar Albarkatun Mai, Diezani Alison-Madueke.

EFCC ta ce ta gano kudaden ne a asusun Diezanni da bankin Fidelity a Najeriya.

Bayan haka kuma hukumar ta cafke tsohon daraktan bankin mai suna, Nnamdi Okonkwo, wanda a yanzu na daya daga shugabannin bankin ‘First Bank’ wanda a baya ya sha tambayoyi kan Dala miliyan 153 da kuma Dala miliyan 115.

Duk da cewa EFCC ta karbi Dala miliyan 153, har yanzu batun Dala miliyan 115 da a ke zargin shi a kansu na gaban kotu. Inji Aminiya.

A yanzu dai Mista Okonkwo da Charles Onyedibe na hannun EFCC inda suke amsa tambayoyi kan Dala miliyan 72.8 da aka samu a asusun Diezani.

Ko a watannin da suka gabata sai da gwamnatin tarayya ta yi gwanjon wasu kadarorin da ta gano daga Diezani.

Tun bayan saukar ta daga kujerar minista, Diezani ke shan tuhume-tuhume kan zargin badakala da dukiyar kasa.

 

nigeria.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp