fidelitybank

EFCC ta bankaɗo makarantar da a ke koya wa Matasa zamba ta Intanet

Date:

Hukumar yaƙi da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ce ta kama mutum 25 waɗanda take zargin masu damfara ne ta intanet a wani wuri da ake kyautata zaton wurin horas da damfara ne, a birnin Benin na jihar Edo.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, EFCC ta ce ta samu nasarar yin hakan ne a ranar Alhamis ta hanyar amfani da jami’anta na shiyyar Benin.

Bayanin ya ƙara da cewa “kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri ne da ta tattara, waɗanda ke nuna cewa ana amfani da wani gini a matsayin wurin koyar da damfarar yahoo ko kuma horas da masu son ƙwarewa a sauran hanyoyin damfara ta intanet.

Hukumar ta ce ta kuma gano wasu kaya a lokacin samamen nata, waɗanda suka haɗa da dalla-dallan motoci guda shida, da kwamfutoci da kuma wayoyi.

Najeriya dai ta yi ƙaurin suna a harkar damfara ta intanet a duniya.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp