Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa arziki ta’annati, EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele ranar Laraba saboda ba da izinin buga sabbin takardun naira na miliyan 684.5 a kan naira biliyan 18.96.
Tun farko an tsara gurfanar da shi ne ranar 30 ga watan Afrilu da ya gabata amma aka ɗage ranar bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kotun da kuma ɓangarorin.
A tuhume-tuhumen huɗu da aka shigar a kansa, EFCC ta yi zargin Emefiele ya yi burus da umarnin kotu da nufin jefa jama’a cikin mawuyacin hali lokacin aiwatar da tsarin sauya takardun naira da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi.
EFCC ta kuma zargi Emefiele da ba da izinin cirar naira biliyan 124.9 daga asusun bai ɗaya na ajiyar kuɗaɗen shu=iga na gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa tsohon gwamnan CBN zai gurfana a gaban kotu kan waɗannan tuhume-tuhume gaban mai shari’a Maryann Anenih ta babbar kotun tarayya da ke Abuja.
A ranar 17 ga watan Nuwamban 2023, an gurfanar da Emefiele gaban mai shari’a Hamza Muazu kan tuhume-tuhume shida kan wata badaƙala ta siyan kayayyaki, zargin da ya musanta.
An kuma zarge shi da yin amfani da matsayinsa wajen amincewa da kwangilar siyan motoci 43 a kan kuɗi naira biliyan 1.2 daga 2018 zuwa 2020.
A cikin 8 ga watan Afrilun 2014 ne kuma EFCC ta sake gurfanar da Emefiele tare da Hnery Omoile gaban mai shari’a Rahman Oshodi na kotun sauraron laifuka na musamman da ke zamanta a Ikeja, jihar Legas kan zargin badaƙalar kuɗi ta dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8.
Emefiele dai ya musanta yin badaƙalar.