Jamiāan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Kano, sun kama mutane goma sha uku, 13 da ake zargi da damfarar yanar gizo a unguwar Badawa da ke cikin birnin Kano a jihar Kano.
Hukumar ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X ranar Juma’a.
An kama wadanda ake zargin ne biyo bayan bayanan sirri da ke nuna wata kungiyar da ake zargi da damfara ta intanet da aikata laifukan da suka shafi yanar gizo.
āA yayin da ake kama su, an kwato wasu abubuwa masu laifi daga wadanda ake zargin.
Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike,ā in ji sanarwar.