Ana nema matashi Ibrahim Mohammed mai shekaru 26 a duniya bisa zargin satar motar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC.
Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce ana neman Mohammed ne da laifin sata da kuma mallakar motar hukumar ba bisa ka’ida ba.
Wanda ake zargin, a cewar sanarwar, an ruwaito cewa dan asalin karamar hukumar Jada ne a jihar Adamawa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bukaci duk wanda ke da labarin inda Mohammed yake da ya tuntubi hukumar nan take.
“Duk wanda yake da cikakken bayani game da inda yake to ya tuntubi EFCC ko ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
“An sanar da jama’a cewa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na neman Ibrahim Mohammed kan zargin sata da kuma mallakar motar hukumar ba bisa ka’ida ba,” in ji sanarwar.