Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, na sanya idanu kan masu yunkurin sayen ƙuri’a a zaɓen gwaman Ondo da ke gudana.
Galibi a wasu zaɓukan Najeriya akan samu rahotonnin sayen ƙuri’un masu zaɓe daga wakilan jam’iyyun daban-daban.
Jami’an na ta zagaya rumfunan zaɓen domin lura da wannan ɗabi’a.