fidelitybank

EFCC na neman jami’an CBEX da suka damfari ƴan Najeriya ruwa a jallo

Date:

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ayyana neman wasu jami’an CBEX waɗanda take zargi da hannu a damfarar ƴan Najeriya miliyoyin kuɗaɗe a wani tsarin zuba kuɗi.

Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta ranar Juma’a, ta ce tana zargin mutanen takwas da yaudarar jama’a su zuba kuɗi don samun riba – daga bisani suka tsere da kuɗaɗensu.

Hukumar ta bayyana sunayen mutanen da Seyi Oloyede da Emmanuel Uko da Adefowora Oluwanisola da Adefowora Abiodun Olaonipekun.

Sauran sun waɗanda ta ce ƴan ƙasashen waje ne sun haɗa da Johnson Otieno da Israel Mbaluka da Joseph Kabera da kuma Serah Michiro.

“Muna son sanar da al’umma cewa muna neman waɗannan mutane ruwa a-jallo saboda zargin damfarar mutane a wani tsarin zuba kuɗi na intanet wanda ake kira CBEX,” in ji EFCC.

Hakan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bai wa jami’an EFCC ɗin damar kame da kuma tsare mutanen da aka samu da hannu wajen yaɗa tsarin na CBEX.

tribune newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp