Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC tare da sauran masu ruwa da tsaki sun fara wani zama, domin tattauna batun rashawa da aka samu a babban zaben Najeriya na 2023.
Tawagar, wadda cibiyar ‘The Conversation Africa’ ke ɗaukar nauyin su kamar yadda ta tsara gudanar da irin wadannan taruka domin tattauna tsarin shugabanci.
A cewar sanarwar, sauran mutanen da ake zama da su sun hada da kungiyoyin farar-hula da kungiyar Code4Afrika da dai sauransu.
Ana sa ran bayan kammala zaman a fito da batutuwa na zarge-zarge da ake ta yi kan rawar da rashawa ta taka a zaɓen Najeriya da kuma sauran kalubale da ake zargi.