fidelitybank

EFCC ba ta kama ni ba – Mele Kyari

Date:

Tsohon hugaban kamfanin mai na NNPCL, Mele Kyari, ya musanta rahotanni da ke cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama shi – kan wani bincike da ake yi na zargin almundahanar kuɗi da ya kai dala biliyan 2.9, wanda aka ware don sake gyara matatun ƙasar.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, Kyari ya yi watsi da rahotannin – inda ya ce wasu ne kawai ke son ɓata masa suna.

“A tsawon kwanaki da suka gabata, na samu kiraye-kiraye daga ƴan uwa da abokai kan rahoton da wata jarida ta yaɗa cewa ina tsare a ofishin EFCC.

“Wannan kawai yunkuri ne na ɓata min suna da jaridar da kuma waɗanda suka ɗauki nauyinta ke son yi,” in ji Kyari.

Ya kuma ce a shirye yake wajen faɗar gaskiyar abin da ya gudanar a ofishinsa lokacin da yake shugabancin NNPCL.

“Zan ƙara nanata cewa na riƙe mukamin da aka bisa tsoron Allah, domin ko ban faɗi gaskiya a nan ba, zan faɗa a gaban Allah, in ji shi.

A farkon watan Afrilu ne, shugaba Bola Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin kamfanin mai na ƙasar NNPCL, inda ya maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari.

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp