fidelitybank

ECOWAS za su gana Ghana akan yadda za su yaƙi Nijar

Date:

Manyan hafsoshin sojin Afirka ta Yamma ECOWAS, za su gudanar da taro a ‘yan kwanaki masu zuwa don tsara shirye-shirye kan yiwuwar amfani da ƙarfin soja, yayin da ƙasashen duniya ke ƙara nuna fargaba game da yanayin da ake tsare da hamɓararren Shugaba Bazoum Mohamed.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce taron manyan hafsoshin sojin na nuna cewa ƙasashen Afirka ta Yamma suna gaggauta shirye-shiryen tura sojoji da yiwuwar ɗaukar matakin kawar da masu juyin mulki a Nijar.

“Ana tsara yin wani (taron) a makon gobe,” Reuters ya ambato wani mai magana da yawun Ecowas yana cewa.

Wani jami’in gwamnatin Najeriya da kuma wata majiyar sojojin Kwatdebuwa sun ce za a yi taron ne ranar Asabar a Ghana.

Zuwa yanzu babu masaniya ƙarara kan yadda girman rundunar zai kasance, da tsawon lokacin da za a shafe kafin a iya tattaro dakarun, da kuma idan haƙiƙa rundunar za ta auka don yin mamaye.

Ƙungiyar Ecowas dai ta ce har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke kuma tana fatan za a iya cimma masalaha cikin lumana. Masu sharhi kan al’amuran tsaro kuma sun ce dakarun Ecowas na iya kwashe tsawon makonni ko fiye da haka, kafin su haɗu, abin da mai yiwuwa zai ba da dama ga ƙoƙarin tattaunawa.

Kwatdebuwa ce kaɗai ƙasar da ya zuwa yanzu ta bayyana adadin dakarun da za ta aika. Shugaba Alassane Ouattara ya yi alƙawari a ranar Alhamis cewa ƙasarsa za ta aika wata bataliyar sojoji da ta kai yawan mutum 850 – 1,100. In ji BBC.

Hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum ya kasance juyin mulki na bakwai a Yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekara uku, abin da kuma ya ƙara jefa yankin cikin tunzuri, baya ga hare-haren masu iƙirarin jihadi da yake fama da su tsawon lokaci

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp