fidelitybank

ECOWAS ta bayar da dala miliyan 25 a yaki ‘yan ta’adda a Najeriya da Nijar

Date:

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ware dala miliyan 25 da zimmar yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da Burkina Faso.

Ecowas ta tsara kashe kuɗin ne a shekarar 2024, kamar yadda Kwamashinar Raya Al’umma ta Ecowas Farfesa Fatou Sarr ta bayyana a hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja yau Juma’a.

Farfesar ta ce an ware miliyan huɗu daga cikin kuɗin don ayyukan agaji musamman ga mutanen da bala’o’i suka shafa.

“Haka nan, Ecowas ta ware dala miliyan ɗaya da zimmar daidaita rayuwar mutanen da ta’addanci ya shafa, kamar ‘yan gudun hijira da kuma waɗanda aka ji wa rauni,” in ji ta cikin rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.

Ta ƙara da cewa a 2023 kaɗai, Ecowas ta ba da tallafin dala miliyan 12.6 ga mutane sama da miliyan huɗu da ta’addanci ya shafa a yammacin Afirka

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp