Yau Asabar ne kuma Shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS ko CEDEO za su gudanar da taro a Abuja babban birnin Najeriya.
Yankin na yammacin Afrika na fuskantar barazanar rashin haɗin kai tun bayan da ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar suka bayyana aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar.
Yayin da a ɗayan ɓangaren ƙasar Senegal ke fama da dambarwar siyasa sakamakon matakin shugaba Macky Sall na ɗage babban zaɓen ƙasar.
Ana saran dai a wanann taro ƙungiyar za ta lalubo mafita kan wadanan matsaloli da suka mamaye yankin.
Wannan zai iya zama gagarumin ƙalubale da kungiyar ke fuskanta tun bayan kafata shekaru 50 da suka gabata.
Hudu cikin mambobin ƙungiyar 15 yanzu haka na ƙarƙashin shugabancin soji.
Taron kuma na zuwa ne bayan da tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, kuma shugaba ɗaya tilo da ya rage cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar ta ECOWAS ko CEDEO, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya yi kira da a gaggauta ɗage duk wani takunkumin da aka ƙaƙaba wa ƙasashen Gini da Burkina Faso da Mali da kuma Nijar.