fidelitybank

Ebonyi ba za ta taba shiga tsagin Biafara ba – Umahi

Date:

Gwamna jihar Ebonyi, David Umahi ya tabbatar da cewa, jiharsa ba za ta taɓa shiga yunƙurin kafa ƙasar Biafra ba.

Umahi wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki, ya faɗi hakan ne a Abakaliki babban birnin jihar ranar Alhamis yayin wata liyafa da aka haɗa masa.

Kazalika gwamnan ya roƙi hukumomin Najeriya da su murƙushe duk wanda ke son tayar da hankali a yankinsu na kudu maso gabas.

Ya ce, “Abu na farko dai, na sha faɗa, duk wanda ya tambaye ku game da Biafra ku ce Ebonyi ba za ta taɓa shiga Biafra ba. Mu ba ‘yan Biafra ba ne.An wulaƙanta mu a baya kuma yanzu ne muke wartsakewa, amma kuna so mu koma baya. Ba za mu koma ba.

“Na faɗa wa gwamnonin yankin Kudu maso Gabas cewa, mu muna son mafita ne ta hanyar siyasa, sannan kuma duk wanda ya ke son tayar da hankali a murƙushe shi.Babu wani ɗan ƙabilar Igbo da zai zama shugaban ƙasa kuma ba zai so ɗorewar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya ba, saboda muna da dukiya a ko’ina a faɗin Najeriya”. A cewar Umahi.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp