Za a bayar da hutun makarantu nan da mako biyu a Uganda bayan Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar ɗalibai takwas.
Uwargidan shugaban ƙasar Janet Musaveni, wadda ita ce ministar ilimi ta ƙasar ta ce an samu ɗalibai 23 waɗanda suka kamu da cutar ta ebola.
An tsawaita dokar kulle sanadiyyar cutar a gundumomin Mubende da Kassanda, inda nan ne cibiyar ɓarkewar cutar.
Hukumar lafiya ta Duniya ta ce an samu mutum 150 da suka kamu da cutar tun daga cikin watan Satumba, yayin da mutum 64 suka mutu.
Ya zuwa yanzu dai babu rigakafin nau’in cutar da ke addabar ƙasar.


