An dage karawar da Bayern Munich za ta yi da Union Berlin, saboda ruwan dusar kankara a babban birnin Bavaria, kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Asabar.
An shirya gudanar da wasan ne a ranar Asabar da yamma amma sanarwar manema labarai daga Bayern ta ce “hatsarin tsaro da yanayin zirga-zirga ya sanya ba a iya kaucewa.”
Karancin yanayin zafi ya haifar da dusar ƙanƙara a kudancin Jamus, musamman a Munich.
Gabanin soke wasan dai tuni hukumomin sufuri na birnin Munich suka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a yankin mafi girma na Munich, yayin da cunkoson ababen hawa suka tsaya cak.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Bayern ta ce akwai “hadari mara misaltuwa ga ‘yan kallo” kuma ta bayyana “ba shi yiwuwa a isa filin wasa na Arena”.
“A karkashin waÉ—annan sharuÉ—É—an, ba za a iya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro da sauran ma’aikatan filin wasan da suka dace don ci gaba da wasan za su iya zuwa filin wasa na Allianz.”
Shugaban Bayern Jan-Christian Dreesen ya ce “Mun yi nadama sosai cewa muna bukatar soke wasan, amma amincin magoya bayanmu da masu goyon bayan Union Berlin shi ne cikakken fifiko,” in ji shugaban Bayern Jan-Christian Dreesen a cikin wata sanarwa.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Jamus (DFL) da ke gudanar da gasar Bundesliga ta tabbatar da soke wasannin a ranar Asabar kuma ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sabon ranar da za a buga wasan.


