Hukumomin agajin Majalisar Dinkin Duniya da suka yi taro a Geneva, domin cikar mamayar Rasha a Ukraine kwana dari sun fitar da gargadi a kan irin mummnar asarar da Ukraine da ma duniya za su yi sakamakon yakin kasar.
Sun ce akwai kusan ‘yan Ukraine miliyan 16 da suke matukar bukatar taimako.
Haka kuma akwai mutum biliya daya da dubu dari bakwai a fadin duniya da ke fama da karuwar talauci saboda karuwar farashin kayan abinci sakamakon toshe tashoshin ruwan Ukraine da Rasha ta yi.
Shugaban shirin samar da abinci na duniya Mike Dunford ya ce akwai mutum fiye da miliyan takwas da suke da matsalar abinci ga yunwa a Afirka.
Da yake jawabi a fadar gwamnatin Amurka game da tsadar rayuwa, shugaba Biden ya bayyana cewa manyan kalubale biyu ne suke damun duk wasu iyalai a yanzu, wato tashin litar mai da tashin farashin kayan abinci a shaguna.
Kuma dukkan wadannan kalubale yakin da Putin ke yi a Ukraine ya janyo su.Ga farashin iskar ya tashi tun daga farkon shekarar nan ma