Babban bankin Rasha ya bayar da umarnin dakatar da tallata hannayen jarin ƙasashen waje da kuma waɗanda ke son sayar da hannun jarinsu na Rasha.
Wannan na zuwa a yayin da darajar kuɗin Rasha na rubble a kasuwannin nahiyar Asiya ta faɗi da kashi uku bisa huɗu
Farashin ɗanyen mai ya yi sama da kusan kashi huɗu cikin 100.
Ƙasashen yammaci sun ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai a matsayin martani ga da yaƙin da ta ƙaddamar a Ukraine.