fidelitybank

Dukkannin jami’an mu su janye daga ƙananan hukumomin Ribas – Rundunar Ƴansanda

Date:

Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sandan da aka tura a baya domin rufe kananan hukumomi 23 na jihar Ribas.

An sanar da wannan umarnin ne a ranar Litinin a wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko ta fitar.

Sanarwar ta ce, umarnin ya biyo bayan ci gaban siyasa da aka samu a jihar Ribas.

“Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bala Mustapha, ya mika umarnin babban sufeton ‘yan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun, na gaggauta janye dukkan jami’an ‘yan sandan da aka tura a baya domin rufewa da kuma kare sakatarorin kananan hukumomin jihar.”

Sanarwar ta jaddada cewa matakin “ya yi daidai da kudurin rundunar ‘yan sandan Najeriya na tabbatar da tsaka-tsaki da kuma gudanar da ayyukan dimokuradiyya cikin sauki.

Ya kuma kara da cewa za a sake tura ma’aikata zuwa yankunan ne kawai idan aka samu rikici ko kuma tabarbarewar doka da oda, inda a nan ne za a gaggauta aiwatar da matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta bai wa al’umma tabbacin ci gaba da jajircewarta wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar, yayin da ta kuma jaddada kwazonta wajen gudanar da ayyukanta.

An yi kira ga jama’a da masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda yayin da lamarin ke faruwa.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp