Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce dukkan ma’aikatan Najeriya da ke aiki a ma’aikatun gwamnati ko masu zaman kansu sun cancanci cin moriyar ƙarin albashi mafi ƙanƙanta na naira dubu 70 da majalisar dokokin ƙasar ta amince.
Akpabio wanda ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Talata bayan amince wa da ƙudirin albashin mafi ƙanƙanta ya zama doka, ya ce:
“Idan maɗinki ne kai sai ka ɗauki wasu mutane aiki, ba za biya su abin da ya gaza naira dubu 70 ba. Haka idan ke uwa ce da ke da sabon jaririn da ki ke son ɗaukar wadda za ta kular miki da shi, to ba za ki biya ta albashi ƙasa da abin da doka ta amince shi ne mafi ƙanƙanta ba… dokar ta shafi kowa da komai.
Haka ma idan ka ɗauki direba ko mai gadi, to ba za ka biya su ƙasa da naira dubu 70 ba. Ina matuƙar jin daɗin cewa wannan abu ya zama doka, kuma yanzu mun bar wa masu ɗaukar aiki su yi aiki da dokar.” In ji Sanata Akpabio.
Saɓanin abin da shi shugaban majalisar ya faɗa a zauren majalisar, dokar albashi mafi ƙanƙanta ta 2019 wadda aka yi wa kwaskwarima a 2024 ta fayyace wadanda ya kamata su ci moriya da waɗanda ba za su ci moriyar ba.


