fidelitybank

Duk yanayin da shugaban ƙasa ya ke a rinƙa yi masa addu’a ba zagi ba – Sarkin Musulmi

Date:

Mai alfarma Sarkin Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ƴan Najeriya da cewa da su riƙa yi wa shugabannin ƙasar addu’a duk yanayin da ake ciki, kuma duk yanayin da ƙasar ke ciki.

Sultan ya yi wannan kiran ne a Jami’ar Ilorin a ranar Alhamis a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron ƙaddamar da littafin da aka rubuta a kan shugaban hukumar JAMB Farfesa Is’haq Oloyede, wanda ya yi ritaya daga aikin jami’a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sultan ɗin ya ƙara cewa, “ku daina tsine wa shugabanni duk yadda abubuwa suka lalace, maimakon haka gara ku riƙa musu addu’a. Ku daina faɗin abubuwa marasa kyau a kansu. Duk lalacewar shugaba ku guji tsine masa,” in ji shi.

A nasa jawabin, ministan shari’a Lateef Fagbemi (SAN), wanda shi ne shugaban taron, kira ya yi ga ƴan Najeriya da su riƙa ƙarfafa wa shugabanninsu gwiwa.

“Ban ce babu matsala ba, amma da zarar kun fara ɓata ƙasarku a idon duniya, ban san me muke tuna wa duniya ba game da ƙasar.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp