Gwamnatin Neja ta baiwa ma’aikatan gwamnati da ke son takara a zaɓen 2023 wa’adi su ajiye aiki.
Wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin jihar ta ce gwamna Abubakar Sani Bello ya bayar da umarni ga duk wani ma’aikaci da ke da niyyar takara ya ajiye aikinsa kafin 31 ga watan Maris na 2022.
Gwamnan ta ce wannan na ƙarƙashin dokar zaɓe da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu da ta ce duk wani ma’aikaci ko mai riƙe da muƙamin gwamnati ya ajiye aikinsa kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu.