fidelitybank

Duk wanda zai shigo Najeriya ba sai an yi masa gwajin Korona ba – Boss Mustapha

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ce,, sabbin dokokin yaƙi da annobar korona da ta sauƙaƙa wa matafiya za su fara aiki ne daga gobe Litinin, a cewar shugaban kwamatin yaƙi da korona na shugaban ƙasa Boss Mustapha.

Sabbin dokokin da kwamatin ya fitar sun ƙunshi cewa, duk wanda ke son shiga Najeriya ba sai ya yi gwajin cutar na shigowa ba da kuma bayan sauka matuƙar dai an yi masa rigakafin cutar.

Su ma yara ‘yan ƙasa da shekara 18 za su samu wannan alfarmar ko da ba a yi musu rigakafin cutar ba.

Sai dai kuma, masu son shiga ƙasar da ba a yi wa rigakafin ba, ko kuma ba su samu cikakkiya ba, har yanzu dole ne sai sun yi gwaji kwana biyu kafin su shiga sannan kuma su yi na bayan sauka, da kuɗinsu.

A gefe guda kuma, dukkan fasinjojin da ke son zuwa Najeriya sai sun yi rajista a shafin matafiya na gwamnati a adireshin NITP– https://nitp.ncdc.gov.ng.

‘Yan Najeriyar da ke son zuwa ƙasashen waje kuwa, an shawarce su da su yi rigakafin sannan kuma su san dokokin ƙasashen da za su je na yaƙi da korona kafin su tafi.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp