Gwamnan jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, ya bayyana cewa digiri na biyu shi ne mafi karancin cancantar karatu ga duk wanda ke son koyarwa a makarantun sakandaren jihar.
Gwamnan ya bayyana shirye-shiryen da gwamnatinsa ta yi na fannin ilimi a lokacin wani liyafar cin abincin dare da manema labarai a Jalingo a ranar 7 ga watan Janairu.
A cewarsa, mafi karancin cancantar karatun malaman makarantun firamare shi ne matakin digiri na farko a jami’a, yana mai jaddada cewa nan ba da dadewa ba ne za a kammala takardar shedar karatu ta kasa NCE a matsayin mafi karanci ga malaman firamare.
Ya yi nuni da cewa, za a sake dawo da karatun Tarihi a matsayin darasi a cikin manhajar ilimi na farko tun daga makarantun firamare a jihar.
Kefas ya ce; “Za mu dawo da karatun Tarihi a makarantunmu na firamare da sakandare da ke jihar domin kafa ginshikin ci gaba cikin sauri.
“Ba da nisa ba, dole ne malaman firamare a jihar su zama masu digiri na farko yayin da malaman makarantun sakandare su sami mafi karancin digiri na biyu don inganta ilimin jihar.
“Wannan shi ne babban dalilin da ya sa muka rage kudin makaranta ga daliban da suka kammala digiri a jami’ar jihar. Dole ne mu tabbatar da kyakkyawar makoma ga yaranmu. Manufarmu ta ilimi kyauta ba abin wasa ba ne kuma duk wanda ya tsaya kan hanyar cimma hakan za a murkushe shi.”
Gwamnan ya yi kira ga ‘yan jarida da su sanya ido kan yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da manufofin ilimi kyauta a makarantun firamare da sakandire domin tabbatar da cewa dukkan shugabannin makarantun suna yin abin da ya dace.


