Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya bayar da umarnin kama duk mutumin da ya ƙi karɓar tsofaffin takardun kuɗi a jihar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya fitar, gwamnan ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har zuwa lokacin da kotun ƙolin ƙasar za ta bayar da hukuncin ƙarshe game da ƙarar jihohin arewacin ƙasar uku suka kai gabanta suna ƙalubalantar matakin.
A makon da ya gabata ne dai jihohin Kaduna da Kogi da kuma zamfara suka kai Babban Bankin ƙasar da gwamnatin tarayya ƙara gaban kotun ƙolin ƙasar kan batun wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.
Gwamna Matawalle ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake rantsar da alƙalan babbar kotun jihar da sabbin masu ba shi shawara na musamman a Gusau fadar gwamnatin jihar..
Gwaman ya ce sun je kotun ƙolin ne shi da takwarorinsa gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, inda suka buƙaci kotun da ta bayar da umarnin ƙara wa’adin amfani da tsofafin takardun kuɗin.
Ya ƙara da cewa ”Wannan mataki da kotun ƙoli ta ɗauka ya taimaka wajen kare ƙasar nan daga faɗawa cikin rikice-rikice, waɗanda ka iya shafar zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar, lamarin da zai iya shafar babban zaɓen ƙasa da aka shirya gudanarwa cikin wannan wata”.
Gwamnan ya kuma bayyana farin cikinsa game da ci gaba da amfanin da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar a harkokin kasuwanci da hada-hadar yau da kullum.
“Muna gode wa Allah kasancewar mutane za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin a harkokin kasuwanci domin samun abun biyan buƙatunsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba” in Matawalle.