fidelitybank

Duk wanda yaki karbar tsohon kudi a Jigawa ku kai kararsa – Badaru

Date:

Gwamnatin Jigawa ta ce, har yanzu tsofaffin takardun kuɗi na naira 500 da 1000 da Babban Bankin Najeriya ya ce sun daina aiki, kuma Shugaba Buhari ya jaddada hakan, suna aiki a jihar, har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin matasa da wasanni da kuma al’adu, Ibrahim Mamsa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa a jiya Alhamis.

Gwamnatin Jigawar ta bayyana wannan matsayi ne, da ke zaman bijire wa sanarwar da shugaban ƙasar, wanda a jawabin da ya yi jiya Alhamis ya ce naira 200 ce daga cikin takardun uku na 200 da 500 da 1000 za ta ci gaba da aiki, har zuwa ranar 10 ga watan Afirilu na wannan shekara.

Sanarwar ta ce gwamnati ta samu labarin cewa wasu mutane da kamfanoni (bankuna) ba sa karɓar takardun tsofaffin kuɗin a jihar kuma hakan ya dame ta.

Gwamnatin ta buƙaci jama’ar jihar da su kai rahoton duk wani ɗan kasuwa ko wani kamfani ko banki da suka ƙi karɓar tsofaffin takardun kuɗin na naira 200 da 500 da kuma ga hukumar da ta dace a jihar.

Gwamnatin Jigawa na cikin jihohi tara da suka bi sahun gwamnonin jihohin Kaduna da Zamfara da Kogi wajen kai ƙarar gwamnatin tarayya Kotun Koli kan batun canjin kuɗin da Babban Bankin ƙasar ya yi.

Shi ma gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya umarci jama’a a jiharsa su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin.

besda salary

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp